An fara gasar Al-ƙur’ani na ƙasa da ƙasa a ƙasar Saudiyya

0
252

A ranar Juma’a ne za a fara gudanar da gasar Al-ƙur’ani mai tsarki na ƙasa da ƙasa a duk shekara a ƙasar Saudiyya tare da wasu kyaututtukan da suka kai Naira miliyan ɗari takwas.

Taron ƙarawa juna sani da karatun Al-ƙur’ani mai tsarki karo na 43 na ƙasa da ƙasa, zai gudana ne a babban masallacin juma’a mai tsarki na addinin musulunci a birnin Makkah na tsawon kwanaki 11 tare da halartar ‘yan takara daga ƙasashe 117 na duniya.

Ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta Saudiyya ce ta shirya taron a ƙarƙashin jagorancin Sarki Salman bin Abdulaziz.

Gasar ta bana ta samu darajar jimlar kyaututtukan da ta samu zuwa SR4 miliyan tare da wanda ya lashe kyautar SR500,000, a cewar ministan kula da harkokin addinin musulunci, ƙira da jagoranci Abdelatif Al Alsheikh, babban mai kula da taron.

KU KUMA KARANTA: ‘Yar Kaduna ta lashe gasar lissafi ta ƙasa da ƙasa

“Kwamitocin gasar sun kammala shirye-shiryensu na karɓar ɗalibai 166 da masu rakiya 50 daga ƙasashe 117,” in ji shi a cikin jawabinsa na kafafen yaɗa labarai.

An sanyawa wannan gasa mai martaba sunan marigayi sarki Abdulaziz, wanda ya kafa kasar Saudiyya.

Masarautar, mahaifar Musulunci, tana shirya gasa ta addini da dama. A farkon wannan shekarar ne aka bayar da kyautuka na SR3.3 ga mahardatan kur’ani a wani gasar ƙasa da aka gudanar a ƙasar Saudiyya.

Ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta ƙasar Saudiyya ce kuma ta shirya bayar da lambar yabo ta haddar Alƙur’ani mai tsarki ta Sarki Salman a cikin watan Maris.

Da farko, sama da ɗalibai maza da mata 3,000 daga sassan masarautar sun shiga matakin neman cancantar shiga gasar.

Daga baya, maza 58 da mata 47 ne suka cancanci shiga gasar.

Membobin alƙalan sun saurari waɗanda suka kammala karatun ne inda suka zaɓi maza 18 da mata 18 a matsayin waɗanda suka yi nasara.

Leave a Reply