An ɗaure ɗan kasuwa watanni huɗu a gidan yari saboda aika saƙon kuɗi na ƙarya

0
236

Kotun Majistare a Jos, ranar Juma’a ta yanke wa wani ɗan kasuwa Samuel Jigede mai shekaru 35 hukuncin ɗaurin watanni huɗu a gidan yari bisa samunsa da laifin aika saƙon kuɗi na ƙarya (text alert) bayan ya sayi kaya.

Majistare Shawomi Bokkos, ta yankewa Jigede hukuncin ataƙaice bayan ya amsa laifinsa. Mista Bokkos, ya bai wa mai laifin zaɓin biyan tara da kuma biyan diyya na Naira 15,000 a can na tsawon watanni a gidan yari.

Alƙalin kotun ya ce hukuncin zai zama kange ga sauran masu son yin laifi.

Tun da farko, Lauyan masu shigar da ƙara, Isfekta Ibrahim Gokwat, ya shaida wa kotun cewa an kai ƙarar ne a ranar 11 ga watan Yuli, a ofishin ‘yan sanda na ‘C’ Division Jos ta hannun wani Uzochukwu Nwakasi, mai shigar da ƙara.

KU KUMA KARANTA: Matar da mijinta ya ɗaure a ɗaki ta rasu a Kano

Mai gabatar da ƙarar ya ce mai laifin ya sayi kaya kuma ya aika da saƙon bogi ga masu sayar da su kafin a kama shi.

Laifin a cewar mai gabatar da ƙara, yana da hukunci a ƙarƙashin tanadin dokar Penal Code na jihar Filato.

Leave a Reply