Za mu janye tsofaffin takardun naira a hankali – CBN

0
233

Daga Ibraheem El-Tafseer

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce zai kawar da tsofaffin takardun kuɗin naira “a hankali” tare da maye gurbinsu da sababbin.

Muƙaddashin gwamnan CBN, Folashodun Shonubi, ne ya bayyana hakan a ranar Talata bayan taron kwamitin kula da harkokin kuɗi na bankin (MPC) a Abuja.

“Idan aka buga kuɗi kuma aka fitar da su ana sa ran za a yi amfani da su har zuwa lokacin da za su tsufa kuma har lokacin da babban banki zai janye su ya meye gurbinsu da sababbi, abin da muke yi ke nan”, a cewarsa lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai.

KU KUMA KARANTA: A hankali ya kamata ku aiwatar da manufar kashless – Sarkin Kano ga CBN

“Dole ne mu fitar da tsofaffin takardun kuɗi. Kuma yayin da suke shigowa, ana sarrafa su kuma ana dawo mana da su sannan mu kuma mu sake fitar da su domin maye gurbin tsofaffin da sababbi.”

A watan Oktoban da ya gabata, Gwamnan CBN Godwin Emefiele wanda aka dakatar, ya ɓullo da shirin sake fasalin manyan takardun kuɗi uku na N200 da N500 da N1000.

Leave a Reply