Wata kotun majistare da ke zamanta a Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin a tsare wasu mutane 25 da ake zargi da damfara a gidan gyaran hali bisa samunsu da laifin yin takardun KAROTA na jabu.
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta gurfanar da waɗanda ake tuhuma, waɗanda ba a bayar da adireshin gidansu ba, bisa zarginsu da laifin haɗa baki, da takardun jabu da kuma zamba.
Mai gabatar da ƙara, Tijjani Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Yuli.
KU KUMA KARANTA: Kotu ta hana gwamnatin Kano rushe gine-gine a hanyar Jami’ar Bayero Kano
Ya yi zargin cewa a wannan ranar an kama wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma a lokacin da suke da takardun jabun na KAROTA.
A cewar mai gabatar da ƙara, laifin ya ci karo da sashe na 97, 393 da 321 na kundin laifuffuka na jihar Kano.
Sai dai waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Lauyan waɗanda ake ƙara, Nazifi Rabiu, ya buƙaci kotun da ta bayar da belin waɗanda ake ƙara kamar yadda sashe na 35 s (6), 36 (5) na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima da sashe na 171 (3) na dokar shari’a ta jihar Kano 2019.
Sai dai babban alƙalin kotun, Halima Wali, ta bayar da umarnin a garƙame waɗanda ake ƙara a gidan gyaran hali, sannan ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Yuli domin yanke hukunci kan buƙatar belinsu.
[…] KU KUMA KARANTA: Kotu ta tsare wasu mutane 25 da ake zargi da laifin yin takardar jabu na KAROTA […]
[…] KU KUMA KARANTA: Kotu ta tsare wasu mutane 25 da ake zargi da laifin yin takardar jabu na KAROTA […]
[…] KU KUMA KARANTA: Kotu ta tsare wasu mutane 25 da ake zargi da laifin yin takardar jabu na KAROTA […]