Daga Ibraheem El-Tafseer
Mai tsaron bayan tawagar Faransa, Samuel Umtiti ya koma taka-leda a Lille daga Barcelona.
Mai shekara 29, wanda ya buga wa Lyon tamola kafin ya koma Barcelona, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyu da ƙungiyar da ke buga Ligue 1.
Umtiti – wanda ya taɓa lashe Kofin Duniya – ya sha fama da jinya kusan shekara huɗu, hakan ya sa aka bayar da aronsa da Lecce a kakar da ta wuce.
”Tun farko na so komawa Lyon, daga baya na amince na taka-leda a Lille, wadda ita ce ke buƙatar na buga mata tamola,” in ji ɗan wasan.
KU KUMA KARANTA: An dakatar da ‘yar tseren Najeriya Nwokocha daga wasanni kan amfani da haramtattun ƙwayoyi
Mai tsaron bayan ya fara taka leda a Lyon tun daga matasan ƙungiyar, wanda ya lashe babban kofin gasar ƙwallon ƙafar Faransa a 2012.
Umtiti shi ne ya ci wa Faransa ƙwallo a karawa da Belgium a daf da ƙarshe a 2018, sai dai rabon da ya yi wa tawagar wasa tun 2019.