Waliyin amarya ya sace sadaki ana tsaka da ɗaurin aure a Kano

1
280

Wani al’amari mai kama da almara ya faru a Kano, inda aka zargi wani waliyin Amarya da sace sadaki ana tsakiyar ɗaurin aure.

An sace kuɗin sadakin ne ana tsaka da ɗaurin aure a unguwar Kurna dake birnin Kano.

KU KUMA KARANTA: Ana tuhumar wani Malami da auren mata 75

Neptune prime ta jiyo cewa, an dakatar da ɗaurin auren yayin da kowa ya yi cirko-cirko, bayan da aka nemi sadakin amarya aka rasa.

Sai dai wata majiya ta ce, jim kaɗan da faruwar wannan lamari ne sai aka fara ‘yar caje, inda nan da nan aka samu kuɗin a aljihun babbar rigar waliyin amaryar.

Sai dai ya ce, shi fa bai san yadda aka yi kuɗin suka shiga aljihunsa ba.

Daga ƙarshe dai an kori waliyin amarya zuwa waje, sannan aka ƙira ƙaninsa ya maye gurbinsa, aka ɗaura auren.

1 COMMENT

Leave a Reply