NUJ jihar Yobe, ta nuna rashin jin daɗi da ƙara farashi da masu gidajen mai suka yi

Daga Ibraheem EL-TAFSEER

Ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Yobe ta bayyana rashin jin daɗin ta game da halin rashin kishin ƙasa da wasu masu gidajen man fetur da ma’aikata suka yi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe da sauran ƙananan hukumomin jihar, dangane da ƙarancin man fetur da aka samu a yau da kuma ƙaruwar farashin mai ɗin, wanda hakan ya jawo dogon layi a gidajen man.

A wata takarda da ƙungiyar ta fitar, wanda shugaban ƙungiyar ‘yan jarida na jihar Yobe, Kwamared Rajab Mohammed da sakatatensa Alhassan Sule Mamudo suka sa wa hanu, ta bayyana cewa, ƙungiyar ta damu matuƙa da halin da ‘yan jihar ke ciki masu son zaman lafiya.

KU KUMA KARANTA: Cire tallafin man fetur ya jawo hauhawar farashin mai a Najeriya

Don haka muna ƙira ga hukumomin tsaro, hukumomin gwamnati, hukumomin da abin ya shafa da duk masu ruwa da tsaki da su gaggauta ɗaukar matakan da suka dace don ganin an kawo karshen wannan mummunan yanayi da ke iya lalata tattalin arziƙin al’umma.

Za mu iya kwatanta shi a matsayin zagon ƙasa ga tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya. Ƙungiyar za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da sanar da ‘yan ƙasar kan duk wani ci gaba mai kyau tare da yin ƙira ga kowa da kowa da su kwantar da hankula domin za a shawo kan lamarin cikin ruwan sanyi.


Comments

One response to “NUJ jihar Yobe, ta nuna rashin jin daɗi da ƙara farashi da masu gidajen mai suka yi”

  1. […] KU KUMA KARANTA: NUJ jihar Yobe, ta nuna rashin jin daɗi da ƙara farashi da masu gidajen mai suka yi […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *