Mutane bakwai sun mutu bayan sun sha shayi a wajen ɗaurin aure a Kano

Mutane bakwai ne ake fargabar sun mutu, wasu da dama kuma sun kwanta a asibiti bayan sun sha shayin da ake zargin an yi shi da wani ganyen garin da aka fi sani da zaƙami a wajen wani ɗaurin aure a Kano.

Zaƙami yana ƙunshe da sinadari mai taɓa ƙwaƙwalwa.

Shedun gani da ido sun ce lamarin ya shafi kusan mutane 50 kuma har yanzu ba a gansu ba.

Lamarin ya faru ne a unguwar Sheka da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a cikin birnin Kano.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, Sanusi Yahaya, wanda kuma ɗan uwa ne ga amaryar, ya ce ana zargin shayin da wasu magunguna daban-daban banda ganyen gida.

KU KUMA KARANTA: Mutune 5 Sun Mutu, 10 Sun Bata A Wani Hari Da Aka Kai A Jihar Benue

Ya ce ya zama ruwan dare ga matasan yankin musamman masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi su riƙa dafa shayi a lokacin bukukuwa kuma suna fakewa a ƙarƙashinsa domin shan ƙwaya.

“Sun dafa shayin kuma su da kansu ba su san adadi da nau’in magungunan da ke ciki ba har wasu sun yi watsi da shi. Amma wasu daga cikinsu sun dage cewa dole ne su sha shayin, suna masu cewa ƙwaƙwalwar su na iya ɗauka.

“Bayan shan shayin, mutane biyu sun mutu, wasu sun murmure yayin da wasu ke kwance a asibiti,” in ji shi.

Wani shaida Abdullahi Muhammad ya ce ya zuwa ranar Talata mutane bakwai ne suka mutu. Ya ce wasu daga cikin waɗanda ke kwance a asibiti ba ’yan unguwar ba ne amma suna wucewa ne kawai suka yanke shawarar shan shayin.

“Ba mu san ainihin adadin ba a yanzu, amma da safe an tabbatar da mutuwar bakwai.

Wasu ma ba a gayyace su zuwa ɗaurin auren ba, sun zo ne domin su yi kwalliya su sha kwaya,” inji shi.

Ba a iya samun angon don jin ta bakinsa game da lamarin saboda an ce ya gudu tare da wasu.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura domin ba a samu lambarsa ba.

Har yanzu dai bai amsa saƙon da aka aike masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


Comments

One response to “Mutane bakwai sun mutu bayan sun sha shayi a wajen ɗaurin aure a Kano”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Mutane bakwai sun mutu bayan sun sha shayi a wajen ɗaurin aure a Kano […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *