Hamshaƙin ɗan kasuwa Ɗangote, ya gina babbar matatar mai a Najeriya

2
357

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar babbar matatar mai da hamshaƙin ɗan kasuwar ƙasar Aliko Dangote ya gina.

Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar Bashir Ahmad ya ce za a ƙaddamar da katafariyar matatar man da aka fara ginawa tun shekarar 2016 nan da mako biyu masu zuwa.

Kamfanin Aliko Ɗangote ya gina matatar ne da za ta iya tace gangar mai 650,000 a kowacce rana, da nufin magance shigar da tataccen mai cikin ƙasar, wadda ta fi kowacce ƙasa arziƙin man fetur a nahiyar Afirka.

Bashir Ahmad ya ce Buhari zai ƙaddamar da matatar mai ɗin a Legas ranar 22 ga watan Mayun da muke ciki, kafin wa’adin sauƙarsa daga mulki.

Mai magana da yawun Ɗangote ya tabbatar da lokacin ƙaddamar da matatar, to sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

Ana tunanin matatar ta laƙume kuɗi kimanin dala biliyan 19 fiye da yadda aka yi hasashen za ta laƙume tun farkon fara ginata, sakamakon jinkirin shekaru da aka samu wajen ginata.

2 COMMENTS

Leave a Reply