Yadda matar shahararren ɗan ƙwallon ƙafa Achraf Hakimi tayi biyu babu

0
844

Matar shahararren ɗan ƙwallon ƙafar nan, Achraf Hakimi ɗan Maroko dake bugawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG ƙwallo, ta shigar da ƙarar neman saki tare da buƙatar a ƙwace rabin dukiyarsa a bata, sai dai kash duk abin da ya mallaka ya mallake shi ne da sunan mahaifiyarsa ba da sunan sa ba.

KU KUMA KARANTA: Matashi ɗan shekara 15 ya kashe abokinsa akan ƙwallon sunuka

Ana biyan sa fam na Ingila har miliyan ɗaya duk wata (Daidai da Naira miliyan ɗari biyar da saba’in a (farashin gwamnati) ko miliyan ɗari tara da goma a (kasuwannin bayan fage). Sai dai ana saka kaso tamanin cikin ɗari na wannan kuɗi ne a asusun ajiyar mahaifiyar tasa. Duk lokacin da yake buƙatar wani abu sai ya tambayi mahaifiyar tasa ta saya masa.

A halin da ake ciki, bai mallaki mota, gida, zinare ko kayan sakawa ba da sunan sa. Duk yana saya ne da sunan mahaifiyar sa mai suna Fatima.

Yanzu kotu ta sanarwar da matar tasa cewa ai mijin ta miskini ne a dokance, ba shi da komai balle da har za a gutsura a ba ta.

Leave a Reply