Iran za ta dasa na’urorin ɗaukan hoto don kama matan da ba sa saka hijabi

1
385

Adadin matan da ke take dokar saka Hijabi a ƙasar Iran na ci gaba da ƙaruwa a ‘yan kwanakin nan, tun bayan jerin zanga-zanga da aka yi a lokacin mutuwar wata Baƙurdiya ‘yar shekara 22 mai suna Mahsi Amini, wacce aka zarga da keta dokar.

‘Yan sanda a Iran sun ce za su fara amfani da fasahar zamani a wuraren da jama’a ke kai-komo don ganowa tare da hukunta matan da ke karya dokar saka Hijabi a ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya ta amince da sanya hijabi a makarantun sakandare

Wata sanarwa da hukumomin Iran suka fitar a ranar Asabar ta ce, “za a fara amfani da na’urorin ɗaukan hoto ko kyamara a wuraren da jama’a suke, domin gano masu bijirewa dokar.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “za a riƙa aika wa masu take dokar shaida da kuma saƙo na gargaɗi kan yiwuwar a ɗaukar matakin shari’a akansu idan suka sake take dokar.”

Amini ta rasu ne a hannun ‘yan sanda a lokacin da ake tsare da ita bisa tuhumar karya dokar saka Hijabi.

1 COMMENT

Leave a Reply