An yi kira ga hukumar Lantarki ta YEDC ta inganta yadda take ba da wuta a Yobe

3
304

An yi kira ga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta YEDC, da su inganta aiyukan su a jihar Yobe.Shugaban ƙungiyar ‘yan jarida na Najeriya (NUJ), reshen jihar Yobe, Comrade Rajab Mohammed ne ya yi wannan kiran a ranar Asabar, a lokacin taron ƙungiyar ‘yan jaridar, wanda aka gudanar a Sakatariyar NUJ da ke Damaturu.

Shugaban ƙungiyar ta NUJ, Kwamared Rajab ya ce, matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a faɗin jihar na shafar rayuwar talakawan jihar musamman a wannan lokaci na watan Azumin Ramadana.

KU KUMA KARANTA: Yadda kaka ta cinna wa ɗanta, matar shi da jikokin ta wuta a Ondo

Rajab ya ce “jihar ta shiga yanayin ƙunci saboda ƙarancin wutar lantarki a Damaturu da kewaye. Sannan su yi ta raba takardar wutar lantarki na gaira babu dalili, alhali ba su ba da wutar ba, kuma kuɗaɗen suna yawa”.

“Sakamakon rashin wutar a wannan watan na Ramadan, mutane na sayan Amalanken ruwa a kan kuɗi Naira 500 zuwa 700 wanda a baya ake sayar da shi akan Naira 200 kan kowace kololuwar tsada. Sannan kayayyakin abinci da yawa sun baci a cikin Firji.

Shugaban ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga Hukumomin Gwamnati da ke da alhakin samar da ruwan sha da su nemo wasu hanyoyin samar da kayayyaki ga ‘yan kasa.

3 COMMENTS

Leave a Reply