Rikicin Kutep da Fulani, an kashe mutane 8 a Taraba

2
256

Aƙalla mutane takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon rikici da ya ɓarke tsakanin Kutep da Fulani makiyaya a ƙauyukan Kwe Sati da Fikye dake ƙaramar hukumar Ussa a jihar Taraba.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abdullahi Usman, ya tabbatar wa wakilinmu kisan, ya ce ƙila adadin waɗanda suka mutu ya zarce haka.

Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, kakakin ‘yan sandan ya ce lamarin na baya-bayan nan ya faru ne a sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin makiyaya da ƙabilar Kutep.

KU KUMA KARANTA: Yadda Attajiri ya rasa dukiyarsa ya zama mai ga ruwa saboda rikicin boko Haram

“An yi rikicin ƙabilanci tsakanin Kuteps da Fulani. Lamarin ya faru ne a makon da ya gabata, kuma an tabbatar da mutuwar aƙalla mutane takwas.

“Akwai wani harin da ba zan iya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba a halin yanzu saboda ana ci gaba da gudanar da bincike,” in ji Mista Usman.

Kakakin ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa al’amura sun koma kamar yadda aka saba, kuma mutane sun fara komawa gidajensu. A halin yanzu, shugaban ƙaramar hukumar Ussa, Abershi Musa, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Ya zargi gwamnatin jihar da gaza ɗaukar mataki kan kashe-kashen da ake zargin Fulani makiyaya ne suka yi a yankin Kutep.

2 COMMENTS

Leave a Reply