Fashewar bututun ɗanyen mai yayi sanadiyar mutuwar mutane 12

Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta tabbatar da cewa mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar magudanar mai a safiyar Juma’a a yankin Rumuekpe da ke ƙaramar hukumar Emoha a jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko, ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, inda ta ce shaidar farko ya nuna waɗanda abin ya shafa na ɗiban ɗanyen man ne a lokacin da wurin ya kama wuta.

KU KUMA KARANTA: Kwastam ta kama tramadol ɗin naira miliyan 306 a Kaduna

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro cewa, hakan ya afku ne a yayin da wata motar bas ɗauke da ɗanyen mai ta kama wuta, yayin da take barin wurin zuwa wata matatar mai ta haramtacciyar hanya a yankin.

“Ya zuwa yanzu mutane 12 ana kyautata zaton sun ƙone kurmus. Har yanzu ba a gama sanin sunayen waɗanda abin ya shafa ba,” inji ta.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *