An kama ‘yan uwa biyu da laifin kashe mai keken adaidaita

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, a ranar 9 ga watan Fabrairun 2023, ta kama wasu ‘yan uwan ​​juna biyu, Damilola Famoriyo ‘ mai shekaru 34 da kuma Akinbayo Emmanuel Abiodunn, mai shekaru 31, bisa laifin yi wa wani mai suna Amos Oyemechi Chuckwuka fashin babur ɗinsa na adaidaita, suka kuma kashe shi suka jefar da gawarsa a bakin kogi a garin Ijebu-ode.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Abinbola Oyemi ne ya bayyana haka, inda ya ce an kama waɗanda ake zargin ne biyo bayan wani bayani da ‘yan sandan da ke sashin Obalende, a Ijebu Ode suka samu a ranar 13 ga watan Disamban 2022, cewa an tsinto gawar wani mai keke Napep a bakin kogi a unguwar Agoro a Ijebu Ode.

“Bayan samun wannan bayanan, DPO Obalende, SP Murphy Salami ya jagoranci jami’ansa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka gano cewa marigayin ya matuƙin babur ɗin adaidaita ne, wanda ake ta neman gawarsa, daganan kuma ya yi cikakken bayani game da tawagarsa da gudanar da bincike na fasaha da na shari’a na abin da ya faru don gano waɗanda ke da hannu a wannan aika aika.

“Oyeyemi ya ƙara da cewa ƙoƙarin da ‘yan sanda suka yi ya haifar da sakamako mai kyau a ranar 9 ga watan Fabrairun 2023, yayin da ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, Damilola Famoriyo, wanda ke zaune a yanki.

KU KUMA KARANTA: Yadda ƙarancin naira ya haddasa rikici a Ogun

Awosan Fakale da ke Ikorodu a Legas aka kama shi da wayar marigayin. “Kame shi ya sa aka kama wanda ake zargin na biyu, wanda kuma dan uwansa ne mai suna Akinbayo Emmanuel Abiodun da ke zaune a Road 1, Block A, Maya a Ikorodu, Jihar Legas.

“A yayin da ake yi musu tambayoyi, mutanen biyu sun amsa laifin da suka aikata a cikin bayanan da suka bayar, inda suka amsa cewa su ’yan ƙungiyar mutum 2 da suka ƙware wajen ƙwace babura da babur mai ƙafa uku, sun kuma kara da cewa a ko da yaushe suna gudanar da aikin fashi da makami a Ijebu ode da kewayenta.

“A cewarsu, a ranar 13 ga watan Disamban 2022, sun kama Amos Oyemechi Chuckwuka wanda suka yau dara da zummar zai ɗauko masu kayan amfanin gonar su daga yankin Agoro zuwa cikin gari, bayan sun amince akan farashin kuɗin da zasu ba shi.

“Amma da suka isa hanyar Agoro/Ikangba suka tare shi suka kwace masa babur mai ƙafa uku, a lokacin ne marigayin ya yi ƙoƙarin yin kokawa da su, suka yi ta sadarwa har ya mutu, suka ja gawarsa zuwa bakin kogi inda suka jefar da ita.

“Sun ƙara sanar da ‘yan sanda cewa sun yi awon gaba da babura uku masu ƙafa uku a unguwar Ijebu ode, kuma masu sayan su na zaune a yankin Ikorodu a jihar Legas. Abinbola Oyeyemi ya ƙara da cewa “An sami wayoyin marigayin guda biyu a wajen waɗanda ake zargin, da kuma addar da suka yi amfani da su wajen kashe shi.

A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, CP Frank Mba, ya bayar da umarnin a miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda a jihar domin gudanar da bincike cikin gaskiya.


Comments

2 responses to “An kama ‘yan uwa biyu da laifin kashe mai keken adaidaita”

  1. […] KU KUMA KARANTA: An kama ‘yan uwa biyu da laifin kashe mai keken adaidaita […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: An kama ‘yan uwa biyu da laifin kashe mai keken adaidaita […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *