An tsinci gawar-wakin matan Sarkin Mutum biyu da ke jihar Taraba, mai Shari’ah Sani Muhammad su biyu da yaransa biyar da aka yi garkuwa dasu tun a watan Janairun wannan shekarar.
In zaku iya tunawa dai, wasu da ake zargin ‘yan garkuwa da mutane ne sun kai farmaki gidan sarkin na mutum biyu ne dake Jalingo a jihar Taraba ranar 19, 1, 2023 inda sukayi garkuwa da Jama’ah da dama tare da iyalan sarkin sama da mutum 8 inda wani yaro ɗan shekaru 14 daga cikinsu ya tsira ya dawo gida kamar yadda mai magana da yawun ‘yan sanadar jihar Abdullahi Usman ya bayyana.
An samu gawar-wakin ne a ƙauyen Daka da ke ƙaramar hukumar Bali ta jihar Taraban a safiyar jiya Asabar 4/1/2023.
Sarkin na garin mutum biyu ya tabbatar da faruwar hakan inda yace za’a gudanar da jana’izar iyalan nasa ne a garinsa na Mutum Biyu.
Gwamnatin jihar Taraba ta bakin mai magana da yawun gwamnatin jihar Lois Emmanuel ta jajantawa sarkin tare da addu’ah da fatan Allah ya jikan waɗanda wannan lamarin ya rutsa dasu da kuma ta’aziyya ga Sarkin da Jama’ar garin na mutum biyu baki daya.