Yadda masu shirya garkuwa da mutane a yanar gizo suka yi wa wata mata fyaɗe

1
486

Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta fasa wata ƙungiyar ‘yan kasuwa ta yanar gizo, wadda suka ƙware wajen lallasa mata, garkuwa da mutane da fyade don karɓar kuɗin fansa.

Rundunar ‘yan sandan ta ce jami’an leken asirin ‘yan sandan sun kama wasu ‘yan kungiyar guda biyu a wurare daban-daban a ƙananan hukumomin Igwurita da Choba, Ikwerre da Obio/Akpor na jihar.

Mai magana da yawun rundunar, Grace Iringe-Koko, ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal a ranar Laraba.

Iringe-Koko ta ce waɗanda ake zargi, Ikechi Promise da Darlington Obi, sun yaudari ‘yan matan ta hanyar neman ƙulla alaƙa tare da tattaunawa a wani shahararren dandalin sada zumunta na yanar gizo na Tinder.

Ta ce, sa’a ta suɓuce masu ne a lokacin da suka yi wa wata mata mai shekaru 28 da haihuwa irin wannan dabara, inda suka yi awon gaba da ita zuwa Chokocho da ke Fatakwal.

A cewar mai gabatar da rahoton ‘yan sandan, ɓarayin sun yi wa matar fyade, inda suka sace mata wayoyin iPhone guda biyu da wayar Samsung, sannan suka karɓi kuɗin fansa naira dubu 600 daga hannun ‘yan uwanta kafin su sake ta.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ayyukan sashen leken asiri na rundunar, a ranar 6 ga watan Janairun 2023, da misalin karfe 8:30 na dare, inda suka kama wani Ikechi Promise, mai shekaru 30, da Darlington Obi, mai shekaru 35.

“Kamen na su yana da nasaba ne da aika-aikar da suka yi kwanan nan a ranar 20 ga Disamba, 2022, da misalin karfe 7:45 na yamma, lokacin da wata mata mai shekara 28 ta kama hanyar zuwa Mahaɗar Kasuwar Igwurita, aka yi awon gaba da su zuwa bututun Chokocho.

“Waɗanda ake zargin sun amsa cewa tsarin da suke yi shi ne su jawo ‘yan mata ta hanyar tattaunawa kan manhajar Tinder don ƙulla dangantaka.

“ Shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane, Promise Nwaobiri, mai shekaru 32, an bi sawunsa tare da kama shi a unguwar Choba, kusa da Fatakwal, a ranar 9 ga Janairu, 2023, da misalin karfe 1 na rana.

Kakakin ‘yan sandan ta ce ana samun ƙaruwar mace-mace ta hanyar yaudara da yin garkuwa da mutane ta kafafen sada zumunta.

Iringe-Koko ta shawarci ‘yan mata da su yi taka-tsan-tsan wajen ƙulla alaka a shafukan sada zumunta da za su buƙaci su yi balaguro don saduwa da mutanen da ba su sani ba.

1 COMMENT

Leave a Reply