Boka ya mutu a otal yana tsaka da lalata da matar fasto

1
272

Wani boka mai matsakaicin shekaru mai suna Kehinde ya faɗi ya mutu bayan da ake zarginsa da yin lalata da wata mace a wani otal da ke Ikere-Ekiti, a ƙaramar hukumar Ikere ta jihar Ekiti.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin sanannen boka ne da ke bada maganin gargajiya a yankin, kuma ya mutu ne a ranar litinin a ɗakin wani otal da ya ziyarce shi tare da ƙawarsa.

Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto ba a tantance sunan matar ba, sai dai majiyoyi sun ce matar matar wani fasto ce, wato limamin a ɗaya daga cikin coci-coci da ke yankin.

KU KUMA KARANTA:Wata mata ta kashe saurayinta a Otel a Nasarawa

Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce, “Abin da zan iya cewa shi ne, mutumin ya mutu ne a ɗakin otal bayan ya yi lalata da matar da aka ce an yi mata irin tsafin nan na Aljanu domin hanata yin lalata da mazan banza.

“Matar ta yi kwarara ihu ne, bayan da ta fahimci cewa mutumin ya faɗi, sai manajan otal ɗin da wasu mazauna wurin suka yi tururuwa zuwa wurin, inda nan take suka garzaya da mutumin asibitin da ke kusa inda aka tabbatar da mutuwarsa.”

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) a jihar Ekiti, ASP Sunday Abutu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Abutu wanda ya bayyana cewa an fara bincike kan lamarin da ya kai ga mutuwar mutumin, sai dai ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun kama matar?

“Eh, za mu iya tabbatar da mutuwar mutumin a ɗaya daga cikin otal a Ikere-Ekiti ranar Litinin.

Tuni dai aka ɗauko gawarsa aka ajiye a ɗakin ajiye gawa.

“Bari in gaya muku da sauri cewa matar da ake magana a kai tana tare da mu yayin da muka fara bincike don gano musabbabin mutuwar mutumin ko akasin haka,” in ji PPRO.

1 COMMENT

Leave a Reply