Abba gida-gida ya sha alwashin doke abokan takararsa na Kano

0
195

Ɗan takarar jam’iyyar NNPP Injiniya Abba Kabir Yusuf da aka fi sani Abba Gida-gida, ya bayyana cewa yana da ƙarfin da zai iya doke abokan karawarsa ya kuma sami damar lashe kujerar gwamnan jihar Kano a zaɓe mai zuwa.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wata takardar manema labarai, mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na hukumar yaƙin neman zaɓen jam’iyar NNPP a Kano, Hisham Habib, inda ya bayyana ɗab takarar jam’iyyar a matsayin wanda ya fi cancantar tsayawa takarar, sakamakon irin gogewar da ya samu, tsawon shekaru, a matsayin kwamishinan ayyuka a zamanin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Dokta Rabiu Musa Kwankwaso.

KU KUMA KARANTA:NNPP ta bukaci a kama shugaban APC na Kano

A cewar Abba Gida-gida “ gogewata ta wuce na sauran masu neman kujerar gwamnan Kano, na kuma bayar da gudunmawa sosai, a matsayina na kwamishinan ayyuka na samar da ci gaban ababen more rayuwa a jihar, wanda shi ne babban nauyi na ma’aikatar ayyuka.

“Sama da kashi 80 cikin 100 na hanyoyin sadarwa da haɗaɗɗen gadar sama da aka gina a Kano gwamnatin Kwankwaso ce ta fara aiwatarwa.

“A matsayina na injiniya da kwamishina ma’aikata, na kula da aikin gina tituna da manyan gadoji, domin tabbatar da cewa sun yi aiki, bisa ka’idojin ƙasa da ƙasa, na inganci, ta hanyar amfani da ƙwarewata a matsayina na kwararren injiniya.” in ji shi.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, za a ƙaddamar da tsare-tsaren ɗan takarar gwamna mai shafuka 70 domin ci gaba da sauya fasalin jihar Kano zuwa wani mataki na bunƙasar tattalin arziki da ci gaban kasa, wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin jihar Kano.

“Shugabannin jam’iyyar NNPP sun zaɓi Abba ne bisa la’akari da ƙwarewarsa da tarihinsa, a matsayin kwamishinan ayyuka a zamanin Dokta Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya sauya Kano sosai zuwa jiha mai ci gaban tattalin arziki.

“Al’ummar Kano, tun daga lokacin suka yi ta kishin kawo sauyi, domin gwamnatin APC ta ɓarnata shekaru takwas, tana tafka almundahana da almubazzaranci da son zuciya, ba tare da wani nasarar da ta samu ba.

“Hakazalika, an rage wa ‘yan fansho kuɗinsu, yayin da ma’aikatan gwamnati suka koma mabarata, kuma tuni fannin ilimi ya gurɓace, sakamakon sayar da harabar makarantar ga ‘yan kasuwa,” in ji sanarwar.

Bugu da kari, sanarwar ta yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a da su yi watsi da duk wani nau’i na kalaman tsoratarwa da jam’iyyar APC ke yi a jihar a daidai lokacin da zaɓen gwamna ke ƙara gabatowa, inda ta tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa jam’iyyar NNPP ta ƙara shiryawa da kuma shirin kwace kujerar gwamnan jihar Kano.

“Gwamnatin Ganduje, a cewar sanarwar, ta kunyata mafi yawan al’ummar Kano, ciki har da matasa da waɗanda suka yi ritaya, yayin da ɗan takarar jam’iyyar na takarar gwamna, ba shi da karfin da zai iya ƙarawa gwamnati daraja, domin shi ne ci gaban gwamnatin Ganduje da ke tada zaune tsaye.” In ji sanarwar.

Leave a Reply