Ina samun aƙalla dubu 80 a wata daga saida kayan ƙamshi: Ɗalibar Jami’a

0
415

Wata ɗalibar jami’ar Modibbo Adama da ke Yola a jihar Adamawa, Raudah Sheik-Jimeta, ta bayyana cewa tana samun naira 80,000 a duk wata daga sayar da kayan ƙamshin da take yi.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito, ɗalibar da ta kammala shekarar ƙarshe na karatun digiri a jami’a na samun kayan kamshin daga manoma na gida.

Raudah Sheik Jimeta, wadda ɗalibar fasahar sadarwa ce ta ce, “Na fara hada-hadar kayan ƙamshi irin su garin chili da citta da man tafarnuwa da ‘Daddawa’ da ake sarrafa su da wake da kamu da kuma garin ɗanwake.

“Na fara kasuwancin ne a shekarar 2020 a lokacin kulle na cutar korona (COVID-19) da jarin iri na N30,000 saboda ina matuƙar son dogaro da kai, domin in taimaki kaina da dangina.”

Ta kuma bayyana cewa mijinta, da ‘yar uwarta ne suka sa ta fara wannan sana’ar. “Ina jin daɗin babban goyon bayan da mata masu bin tallata a dandalin sada zumunta da abokai na gida da ‘yan uwa suke bani.

Burina shi ne na zama sananniya a kowane gida akwai kayan na, na samar da ayyukan yi ga matasa da mata a faɗin ƙasar nan,” inji ta.

Leave a Reply