2023: El-Rufai ya yi gargaɗi kan amfani da ƙabilanci da addini wajen yaƙin neman zaɓe

1
431

Gabanin zaɓen shekarar 2023, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da addini da ƙabilanci wajen yaƙin neman zaɓe.

El-Rufai ya bayyana lamarin a matsayin mai matukar haɗari ga ci gaban dimokuradiyya, inda ya ƙara da cewa, hakan na barazana ga haɗin kan ƙasar.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da hedkwatar ƙungiyar Sultan Foundation for Peace and Development da ke Kaduna, Gwamna El-Rufai, ya ce maimakon amfani da addini da ƙabilanci a wajen yaƙin neman zaɓe, kamata yayi jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa, da kwanciyar hankali na zamantakewa.

KU KUMA KARANTA:El-Rufa’i: mun gaza a matsayinmu na shugabanni a Najeriya

Ya kuma yi kira ga malaman addini da sarakunan gargajiya da su tabbatar da cewa, ‘yan siyasa ba su yi amfani da cibiyoyinsu wajen tallata muradun su wajen kawo cikas ga haɗin kan ƙasa, yana mai cewa abin da ‘yan ƙasa ke buƙata su ne nagartattun ‘yan takara.

A nasa bangaren, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar II cewa yayi gidauniyar na da burin samar da haɗin kai tsakanin Kirista da Musulmi, da kuma bunƙasa ilimi a ƙasar nan, musamman a yankin arewa.

1 COMMENT

Leave a Reply