Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya yi bikin Kirsimeti na bana tare da sojoji a ƙarƙashin rundunar operation haɗin kai a barikin rundunar na Maimalari a Maiduguri, a ranar Lahadi, 25 ga watan Disamba.
A yayin taron, shugaban rundunar sojin (COAS) ya ce sojoji sun fara fatattakar ragowar ‘yan ta’addan boko haram a yankin arewa maso gabas, kuma rundunar sojin ƙasar na kara ƙarfafa haɗin gwiwarsu tare da samar da dabaru domin kawar da ta’addanci da laifukan da suka shafi yankin.
Janar Faruk Yahaya ya umurci hafsoshi da sojojin Najeriya da su kasance masu tsayin daka da kuma ci gaba da yaƙi da ta’addanci. Ya ce rundunar sojin ƙasar na ci gaba da yin amfani da ingantattun dabaru domin tunkarar ƙalubalen rashin tsaro ta hanyar ƙwarewar jami’anta a fagen fama.
Yahaya ya bukaci sojojin da su ci gaba da mai da hankali, da ɗa’a da biyayya ga hukumomin da aka kafa tare da tabbatar da cewa sun fatattaki duk maƙiya kasar nan da kwarewarsu.
KU KUMA KARANTA:Yadda ‘Yar Najeriya ta zama Janar a Rundunar Sojin Amurka
Ya kuma yaba wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da majalisar dokokin ƙasar bisa goyon bayan da suke baiwa rundunar sojin Najeriya domin samun nasarar sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya tanada a sassa daban-daban a faɗin ƙasar nan.
A yayin bikin, an karrama wasu kafafan watsa labarai bisa sadaukar da kai, ga yaki da ta’addanci da tayar da kayar baya, kafafan yaɗa labaran da aka karamma sun haɗar da jaridun Daily trust, Punch,da Leadership, Sai kuma kafar TV na Channels, TVC, NTA da Radio Najeriya.