Mutuwar ma’aikaciya NTA a hatsarin Jirgin ƙasa: Rashin bin ƙa’idar hanyar jirgin ne- NRC

1
441

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), ta yi Allah wadai da hatsarin da jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna yayi a makon da ya gabata, wanda ya murƙushe wata mata, wacce a lokacin ta ke tuƙa mota a kan titin jirgin da ke kan hanyar Chikapere a unguwar Kubwa a Abuja.

Matar da ta rasu, Selimota Idowu, ma’aikaciyar gidan talabijin ta Najeriya ce (NTA), kuma tuni jama’ar yankin suka yi ta cece-ku-ce kan lamarin, sai dai hukumar ta NRC a cikin wata sanarwa da kakakinta Mahmood Yakub ya fitar a jiya ya bayyana cewa an yi wa ababan hawa wurare daban-daban a cikin yankin Kubwa domin samun sauƙi da kuma kare lafiyar su, wanda ba sai sun bi kan titin jirgin ba.

KU KUMA KARANTA: Wata mace ta mutu lokacin da jirgin ƙasa ya murkushe mota a Abuja

Sai dai kuma masu ababen hawan sun ƙauracewa waɗannan hanyoyi guda biyu inda suke yin amfani da hanyar jirgin da hatsarin ya faru, yace ba bisa ƙa’ida ake amfani da wannan hanya ba, waɗanda a ‘yan kwanakin nan suka yi sanadin taho-mu-gama da jiragen ƙasan da ke tafiya a kai” Inji shi.

Hukumar ta NRC ta umurci masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar da su yi amfani da hanyoyi biyu da aka gina a kodayaushe domin kare lafiyarsu “maimakon ketare haramtacciyar hanya da ke kawo babban haɗari ga rayuka da dukiyoyinsu.”

“Muna kira ga manema labarai da su yi amfani da kafafen yaɗa labarai don faɗakar da jama’a kan yadda ya kamata a yi amfani da hanyar wucewa ta layin jirgin ƙasa, manufar gwamnatin tarayya kan sabunta hanyoyin jirgin ƙasa na tabbatar da tsaron masu ababen hawa da jiragen ƙasa ta hanyar gina hanyoyin wuce gona da iri a dukkan ayyukan layin dogo na jirgin,” in ji shi.

1 COMMENT

Leave a Reply