Yadda ‘yar shekara 13 ta haihu bayan tsoho mai shekaru 75 da ke riƙonta ya mata ciki

Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Anambra ta ƙuɓutar da wata yarinya ‘yar shekara 13 da ta haihu bayan da aka yi zargin mai kula da ita, Mista Sunday Muoghalu ya yi mata ciki.

A ƙarshen makon da ya gabata ne, labarin haihuwar jaririn ya bazu a shafukan sada zumunta, inda ya nuna mahaifiyar matashiyar tare da jaririnta a wani asibiti da ke Adazi-Nnukwu a ƙaramar hukumar Anaocha ta jihar Anambra.

An tsare ta ne saboda rashin biyan kuɗin asibiti.

Lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta nemi wata tawagar ma’aikatar mata ta kuɓutar da ita kuma suka ajiye ta a wajen su.

Mai magana da yawun ma’aikatar, Chidimma Ikeanyionwu, a ranar litinin, ya ce an kama Muoghalu a ranar lahadi kuma aka mika shi ga ‘yan sanda.

Matashiyar ‘yar shekara 13 da ta haihu, ta ce ta fito daga jihar Akwa Ibom, yayin da iyayenta suke zauna a Agulu, jihar Anambra.

Ta ce, “Matar Mista Muoghalu ana kiranta Madam Ghana. Hakan ya faru ne lokacin da Madam Ghana ta yi tafiya zuwa ƙauyen su.

KU KUMA KARANTA:An kama likita kan zargin lalata da ‘yar shekara 15, ‘yar uwar matarsa

“Ba ni kaɗai ya yi wa ba, akwai wata yarinya ‘yar shekara bakwai; Mista Muoghalu ya kasance yana lalata da ita ma.

“Wannan ya faru ne lokacin da na fara ganin hailata, sai ya fara tilasta ni na kwana da shi. Na taɓa gaya wa Madam Ghana game da lamarin, kuma ta gargaɗi mijinta, amma da abin ya ci gaba, sai na kasa yin komai.”

Kwamishiniyar kula da harkokin mata da yara ta jihar, Misis Ify Obinabo, ta bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za a gurfanar da mai laifin.

Ta ce, “Idan wanda ake zargin yana da’awar cewa ba shi da laifi, za mu ci gaba da bincike har sai mun gano wanda ke da hannu a ciki.

“Gaskiyar lamarin yayi muni, wani yayi lalata da karamar yarinyar,ya sa ta zama uwa, hakan ba daidai ba ne.

“Don haka, duk wanda ke da hannu a laifin, dole ne a gabatar da shi kuma wannan gwamnati ta himmatu wajen yin hakan.”

Wanda ake zargin, Muoghalu, ya ce shi ne ke da alhakin daukar cikin.
Ɗan shekaru 75 ya bayyana cewa yana wasa ne kawai da yarinyar, bai yi niyyar yi mata ciki ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Tochukwu Ikenga, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *