Anfanin ayaba 12 da ya haɗar da kiyaye lafiyar ƙoda, anfani ga mata masu juna biyu, da taimakawa ƙwaƙwalwar ɗalibai

6
705

1) Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauƙi wajen narka abin da aka ci don ta ƙunshi sinadarin Starch wadda ake samu a cikin Carbohydrates, ba shakka tana taimakawa wajen rage ƙiba, ta yadda jikki zai fara ɗiban wannan starch din a hankali, sannan mutum zai riƙa jin cewa ya ƙoshi, sai ya rage gabzar abincin.

2) Ayaba takan sassautar da hauhawar jini, don tana da sinadarin Potassium, shi kuwa yana da mahimmanci wajen wannan aikin.

3) Zai yi kyau mutum ya sanya ayaba a matsayin ɗan abin da zai rika jefawa a baki lokaci zuwa lokaci kafin cin abinci, ya fi mutum ya ci abin da zai ƙara masa ƙiba, idan ya ji wata ‘yar kasala sai ya janyo guda ya ka ɗa ta a baki ya laƙume ta, ta ma fi wasu juice din da suke dauke da Caffeine, masamman yadda ba ta da sukari sosai don dacewa da ci lokaci-lokaci, kamar in mutum yana wajen aiki, ko tarurrukan da kan dauki dogon lokaci, ko ma lokacin kallon talabijin.

4) Ayaba takan kusan zama wajibi ko don lafiyar hanji, ayaba ƙwara daya tal za ta iya yi wa matum maganin basir, don tana da wani nau’in fibres na masamman wanda yake taimaka wa hanji wurin aikinsa, wannan maganin halittacce ta asali, ta fi ƙara lafiya sama da magungunan Bature, masamman wadan da suke matsaloli irin nasu.

5) Haka zalika ayaba takan sanya kwanciyar hankali da dadin rai, domin tana da sinadarin Tryptophane wanda ɗaya ne daga cikin sinadaran da suke bai wa mutum nutsuwa tare da ba shi kwanciyar hankali na haqiqa, tana daidaita tsarin sinadarin Protein a jiki, don ba wa mutum cikakkiyar lafiya.

KU KUMA KARANTA:Abincin Najeriya da masu neman haihuwa ya kamata su ci

6) In da a ce mutum zai riqa cin ayaba sau uku a rana, wato wajen karin kummalo da wurin kalacin rana ko na maraice to sinadarin Potassium ɗin dake cikinta zai ƙarfafa ƙwaƙwalwarsa, don ɗalibai kuwa yakan yi masu amfani siyasa, don yakan ƙara musu ƙarfin maida hankali sosai a lokacin ɗaukar darasi.

7) Game da mata masu ciki kuwa, ayabar takan taimaka don tana da fa’ida ba ƙarama ba ga mai juna biyu, masamman lokacin da take jin laulayi ko tashin zuciya wanda yake yawan faruwa in cikin yana ƙarami, sannan ayabar za ta iya taimakawa wajen ganin sinadari mai bada kuzari na Glucose da ke cikin jininsu, takan kuma lura da yanayin zafin jiki.

8) Sai kuma zancen cizon sauro, wani in sauro ya cije shi sai ka ga wurin ya yi hulu-hulu, to a irin wannan yanayin za a iya bare ayaba a sanya bawon a wurin, don yakan magance ƙaiƙayin da wurin yakan yi, shi ma wannan ya fi aminci sama da magungunan da mutum zai yi ta shafawa.

9) Ayaba takan taimaka kuma wajen magance ciwon gembon ciki wato Ulcer, ko kuma riga-kafin ciwon, domin takan taimaka wajen ƙanƙantar da sinadarin acid din da abinci yakan bari a cikin tumbi, tawajen daidaita sinadarin acids ɗin narka abincin, da wannan sai ka ga ta yi maganin matsalolin tumbi da dama.

10) Ayaba tana da sinadarin Iron da yawan gaske, ga waɗan da suke da cutar fatarar jini ko Anaemia, don Iron din kan taimaka musamman ga ƙwayoyin jan jini wanda yake kula da dauko Oxygen, ya kuma tabbatar da cewa ruwan jiki wato white blood cell ya ba da gudummuwarsa wajen magance raunuka.

11) Wani abin mamaki game da ayaba hatta gona ɓawonta yana da amfani, don kuwa takan zama taki idan aka kai gona, kenan a maimakon a rika zubarwa sai a kai shi gona inda za a yi aiki da shi don samar da abincin da za mu ci.

12) Ayaba takan taimaka sosai wajen kiyaye lafiyar ƙoda, ta yadda take rage tura Calcium zuwa fitsari, da kuma ƙaranta yuwuwar kamuwa da tsakuwar qoda, kamar yadda bincike ya gano cewa cin Ayaba yakan rage hatsarin kamuwa da kansar qoda, ta yadda aka sami mata wadan da suke cin Ayaba sau 4-6 a sati yadda suka nesanta da kamuwa da kansar ƙoda sama da wadan da ba sa ci, ban da wannan ma sinadarori da dama da suke cikin ayaba sun sanya tana iya kawar da matsalar Ulcer kai tsaye.

Ɗayan plantain

Galibin ayaba har da karkasuwar nau’o’inta duk tana ɗauke da sinadarori kala daban-daban, akwai ma doguwar Ayaba wace yawancinta ba a iya cinya a ɗanya sai an soya ko an gasa ta da wuta, mukan ga ana sanya ta ne a abinci kamar shinkafa, sai a yanyanka ta a dora ta a sama, wato plantain, akan kira ta da Larabci “Mauzul Janna” ita wannan ayaba tana da starch mai yawan gaske, kuma ba ta da sukari mai yawa, ita ma tana da tasiri wajen kawar da maiqo a cikin jini, a taƙaice dai ita ma ayaba ce mai amfani ƙwarai.

Soyayyar plantain