Yadda saurayi da budurwarsa suka binne jaririn da suka haifa da ranshi a Jigawa

0
302

Jami’an ‘yan sanda a jihar Jigawa sun kama wata mata mai suna Balaraba Shehu da saurayinta mai suna Amadu Sale bisa laifin binne jaririn da suka haifa da rai a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce, Balaraba bayan haihuwar jaririn ba tare da aure ba ta haɗa baki da Amadu wajen aikata laifin.DSP Shiisu ya ce an tono jaririn ne daga wani rami da mahaifiyar ta tona a kusa da wani banɗaki a gidansu.

A cewarsa, “A ranar 2 ga Disamba, 2022, da misalin ƙarfe 11:50 rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa wata Balaraba Shehu, mai shekaru 30, daga ƙauyen Tsurma, ƙaramar hukumar Kiyawa, ana zargin ta haihu kuma ta binne jaririn. “Bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sanda suka nufin inda aka aikata laifin.

“Da isowarsu, jami’an tsaro sun ɗauki matakin ne suka zaƙulo jaririn daga wani rami da aka tona kusa da wani banɗaki a gidansu, inda mahaifiyar da ake zargi ta binne shi. An garzaya da jaririn zuwa babban asibitin Dutse, kuma likita ne ya tabbatar da mutuwarsa.

“An kama wadda ake zargin kuma yanzu haka tana hannun ‘yan sanda. “Bincike na farko ya sa aka kama wani Amadu Sale da ake kira Dan Ƙwairo, ɗan shekara 25 a ƙauyen Akar da ke ƙaramar hukumar Kiyawa.

“An zarge shi ne da alhakin yi wa Balaraba cikin shege kuma ta haɗa baki dashi wajen binne jaririn bayan ta haihu,” in ji DSP Shiisu. Jami’in hulɗa da jama’a ‘yan sandan, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Emmanuel Ekot Effiom ya bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifukan na rundunar ‘yan sandan, na SCID da ke Dutse, domin gudanar da bincike mai zurfi.

“Za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu domin su fuskanci fushin doka bayan kammala bincike,” in ji DSP Shiisu.

Leave a Reply