Japan ta lallasa Spain,ta tsallake zuwa zagayen gaba

Japan ta samu nasara a kan Spain da ci 2-1 a daren ranar Alhamis, inda ta samu damar tsallakewa zuwa zagayen gaba.

Ƙasar Asiya da ta fado da ci a karon farko ta farka, bayan da ta jefa kwallon a minti na 48 da fara wasa Ritsu Doan.

Akwai sauran karfin da har yanzu ya rage ga ‘yan kasar Japan, wadanda watakila Spain din ta raina, bayan da suka fara zura kwallo a ragar Alvaro Morata a minti na 11 da taka leda, ta sake zura kwallo a ragar, inda dan wasan tsakiya na Japan, Tanaka ya jefa kwallo a raga wanda kasar sa ta zamo a gaba.

KU KUMA KARANTA:Poland ta tsallake zuwa zagayen gaba da wasa duk da rashin nasara a hannun Argentina

A chan gefen kuma, Costa Rica ta kasa ci gaba da matsin lamba wanda ya haifar da ci 2-1 ba tare da an zura kwallo a raga ba amma Jamus ta yi waje da su inda suka ci 4-2.

Kungiyoyin biyu an bar su a baya kuma za su tafi gida yayin da Japan da Spain suka tsallake.

Tun da farko dai, kasar Belgium,wanda ita ce ta ɗaya a duniya ta buga kunnen doki da Croatia babu ci, sannan Morocco ta lallasa Canada da ci 2-1, inda Croatia ta tsallake zuwa rukunin F.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *