Abinda ya sa aka janye dokar hana ‘yan adaidaita hawa manyyan tituna a Kano

Daga Shafa’atu DAUDA, kano

A yammacin Laraba ne gwamnatin jihar Kano ta janye dokar takaita hanyoyin bi ga matuka babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita sahu, ‘yan awowi kaɗan bayan da dokar ta fara aiki da safiyar ranar.

Shugaban Hukumar karota Baffa Babba Dan agundi ne ya bayyana sanar da janye dokar yayin wani taro da yayi da manema labarai a ofisoshin sa a Kano.

Ya ce “mun janye dokar ne saboda biyayyar da ‘yan adaidaita suka yi ga dokar da kuma kokawar da al’ummar jihar suka yi akan dokar”.

Tun da fari dai an gudanar da zanga zangar rashin goyon bayan dokar na takaita wa ‘yan adaidaita sahu hanyoyin da zasu bi, inda wasu matasa sun ka hau kan titin Hadeja Road kusa da Kwanar Dakata don nuna tirjiya ga dokar hana baburan Adaidaita Sahu bin wasu titunan Jihar.

Matasan da suka hada da matuka baburan da kuma mazauna yankin da suka hada da ɗaliban makaranta da ’yan kasuwa da sauran jama’ar yankin inda suka rufe kan titin suka hana sauran ababen hawa bin hanyar.

Baya ga haka kuma matasan sun yi ta ihu tare da furta kalaman Allah-wadai da matakin na Gwamnatin Jihar ta Kano.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun yi amfani da wannan dama wajen jifan jami’an tsaro tare da ababen hawansu da duwatsu, yayin da wasu suka farfasa manyan motocin da gwamnatin Kano ta tanadar domin maye gurbin baburan masu ƙafa uku.

Haka kuma, ana cikin zanga-zangar sai ga wasu daga cikin motocin da Gwamnatin ta samar da suka maye gurbin baburan da ake yi wa lakabi da Kanawa Bus Service sun iso daidai wurin da ake zanga-zangar, nan da nan kuwa matasan suka fara jifan motocin da duwatsu inda suka farfasa gilasan motocin tare da yi wa fasinjojin da ke ciki rotse.

Sai dai kasancewar akwai isassun jami’an tsaro akan titin wanda aka ajiye su don ko-ta-kwana sun yi kokarin kwantar da tarzomar inda suka kama wasu daga cikin matasan wadanda suke zargin su ne da alhakin assasa zanga-zanga tare da tunzura matasan.

Wasu daga cikin ɗaliban makarantu da ke yankin sun shaida wa wakiliyar Neptune prime cewa sun shiga wannan zanga-zangar ce saboda rasa abin hawan da zai mayar da su gidajensu.

Wani dalibai mai suna Ahmad Ali ya ce, “Kasancewar jarrabawa muke yi ana tashinmu da karfe 11:00 na safe, to amma saboda rashin baburan Adaidaita Sahu gashi har yanzu karfe 12:30 muna kan titin, babu motocin da aka ce su za su dauke mu.
“A gaskiya Gwamnati ba ta kyauta mana ba. Kamata ya yi gwamnati ta yi abin a hankali ba wai kawai cikin kankanen lokaci ace za a kawo doka ta fara aiki ba.”

Shi ma wani matashi da ke cikin masu zanga-zangar wanda ya ki bayyana sunansa, ya shaida wa mana cewa sun yi zanga-zangar ne don sun rasa abin hawan da zai biya musu bukatunsu na sufuri.

“Kin San nan akwai Kasuwar Yankaba to muna yin amfani da baburan Adaidaita Sahu wajen daukar mana kayan gwari da muka saya zuwa wuraren kasuwancinmu, amma kin ga yau saboda wannan doka mun rasa abin da zai daukar mana kayan. Ga shi har rana ta yi,” inji shi.

Neptune prime ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya ce ba shi da masaniya a kan abin da ke faruwa.
Sai dai ya ce da zarar ya bincika zai tuntunbe mu. Amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba mu sami kira daga wajenshi ba.

Yanzu haka dai hankula sun kwanta biyo bayan matakin janye dokar da gwmanati jihar Kano tayi.


Comments

One response to “Abinda ya sa aka janye dokar hana ‘yan adaidaita hawa manyyan tituna a Kano”

  1. […] KU KUMA KARANTA:Abinda ya sa aka janye dokar hana ‘yan adaidaita hawa manyyan tituna a Kano […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *