Kotu ta yankewa IGP hukuncin ɗaurin watanni 3 a gidan yari

1
408

Daga Maryam Sulaiman

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata, ta yanke wa Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya (IGP), Usman Alkali Baba, hukuncin ɗaurin watanni uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin kin bin umarnin kotu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, kotun ta yanke hukuncin inda mai shari’a M. O. Olajuwon ya yanke ya kuma bada umarnin a kai IGP gidan yari, kuma a tsare shi na tsawon watanni uku, ko kuma ya bi umurnin da ta bayar a ranar 21 ga watan Oktoban 2011.

Kotun ta ce “Idan a ƙarshen watanni ukun, wanda ya raina kotun ya cigaba da turjiya,to za a ci gaba da rike shi har zuwa wani lokaci, har sai ya wanke kan shi,” in ji kotun.

Hukuncin da aka yanke wa IGP ya biyo bayan ƙarar da wani jami’in ɗan sanda, Mista Patrick Okoli ya shigar, wanda aka tilastawa yin ritaya daga aikin ‘yan sandan Najeriya ba bisa ka’ida ba.

Mai shari’a Olajuwon ya lura cewa duk da cewa hukumar ‘yan sanda ta PSC, ta ba da shawarar a mayar da Okoli bakin aikin shi,akan hukuncin da kotun ta bayar, IGP, ya ƙi bin umarnin. Kotun ta kuma bayar da umarnin biyan Naira miliyan 10, ga wanda ya shigar da ƙarar, a matsayin diyya na musamman saboda tauye masa hakki da hakkokinsa ba bisa ka’ida ba, a matsayinsa na babban jami’in ‘yan sandan Najeriya daga 1993 zuwa yau.

1 COMMENT

Leave a Reply