Yadda amarya ta kashe kishiyarta akan tsire

1
273

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa an kama wata matar aure da laifin kashe kishiyarta da taɓarya.

Matar da ake zargin ta yi amfani da taɓarya ta bugi kishiyarta lamarin da yayi sanadiyar mutuwarta, acewar rundunar ‘yan sandan lamarin ya faru ne a ƙauyen Gar da ke unguwar Pali a ƙaramar hukumar Alkaleri.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, ya ce mijin wacce ake zargin ne ya kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sandan yankin Maina-Maji a ranar 22 ga Nuwamba, 2022.

Ya ce, “A ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, wani Ibrahim Sambo magidanci mai shekaru 40 m, da ke unguwar Gar kauye Pali, karamar hukumar Alkaleri, ya zo ofishin ‘yan sanda ta Maina-maji, inda ya kai rahoton cewa, da misalin ƙarfe 12:00 na safe matar sa ta biyu Maryam Ibrahim mai shekaru 20 ta shiga ɗakin matar sa ta farko mai suna Hafsat Ibrahim mai shekaru 32 ta buge ta da taɓarya a kai.

“A sakamakon haka, wadda aka kwaɗawa taɓaryar ta samu munanan raunuka, an kuma an ɗauke ta zuwa cibiyar kula da lafiya a matakin farko da ke ƙauyen Gar inda likita ya tabbatar da mutuwarta.

“Bayan samun rahoton, wata tawagar jami’an ‘yan sanda da ke aiki da rundunar ta dauki matakin damƙe wacce ake zargin

“Lokacin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amince da aikata laifin, inda ta bayyana cewa a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin ƙarfe 11:00 na safe, marigayiya (Hafsat Ibrahim), ta aiki da ɗanta, Abdulaziz Ibrahim mai shekaru 5 da tsire don ya ba ta (Maryam).

” Ita kuma bayan ta cinye naman sai ta fara jin ciwon ciki, har tayi aman naman. “Bayan nan, (wanda ake zargin) ta kira wata Fa’iza Hamisu, wadda duka gidansu ɗaya, matar ƙanin mijinta, ta gaya mata ainihin abin da ya faru.

“Ta ƙara da cewa Fa’iza ta fada mata cewa kila ciwon ulcer ne, sannan ta ba ta maganin ulcer. “Daga baya, wadda ake zargin ta je cikin ɗakinta, ta ɗauko taɓarya, sannan ta shiga ɗakin uwargidanta a lokacin da take barci ta buga mata taɓarya a kai, har ta mutu.”

1 COMMENT

Leave a Reply