Za a ƙara kudin shiga jirgin ƙasan na Abuja zuwa Kaduna

1
451

Ministan sufuri na Najeriya Mu’azu Sambo ya bayyana cewa za a yi ƙarin kuɗin tikitin jirgin ƙasan da ke zirga-zirga tsakanin babban birnin tarayya Abuja zuwa Kaduna.

Ministan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a sa’ilin da aka yi gwajin jirgin a shirye-shiryen da ake yi na dawo da sufurin jiragen ƙasa a Arewacin Najeriya tun bayan da aka dakatar da hakan a sakamakon matsalar tsaro.

Ma’azu Sambo ya ce za a yi ƙarin ne saboda sauyin da aka samu na tattalin arziƙin qasa.

Ministan ya ce ma’aikatar sufuri na tattaunawa da hukumar lura da jiragen ƙasa ta Najeriya domin ganin ko za a yi ƙarin farashin ne nan take ko kuma sai nan gaba.

Ya ce “kowa ya san farashin kayayyakin masarufi sun tashi, hatta farashin tikitin jiragen sama ya tashi, me zai sa mutane su yi surutu idan an ƙara farashin tikitin jirgin ƙasa?” inji shi.

1 COMMENT

Leave a Reply