Yadda aka kama Mr 442 da abokinsa da takardun bogi a Nijar

Hukumomin ƙasar jamhuriyar Nijar sun ce sun fara bincike kan yadda mawaƙan nan biyu ‘yan Najeriya suka mallaki takardun bogi na ƙasar.

Zuwa yanzu mahukuntan ƙasar Nijar na ci gaba da tsare Mubarak Abdulkareem wanda aka fi sani da 442 da manajansa Orler of Kano a gidan yarin birnin Yamai inda suke zaman jiran kammala bincike kamar yadda babban mai shigar da ƙara na gwamnati ya shaida wa manema labarai.

Babban mai shigar da ƙara a ƙasar ya ce babban laifi ne yin amfani da takardun bogi a jamhuriyar Nijar , ya ƙara da cewa sun bayar da umarni a gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin gaskiya game da lamarin.

Ya ce ”Duk wanda aka samu da laifi za mu tasa ƙeyarsa zuwa gaban kotu, ba za mu yadda wasu su riƙa amfani da takardun ƙasarmu ta hanya wadda take ba ta gaskiya ba, kuma nan gaba duk wanda aka kama da irin wannan laifin to ya kuka da kanshi”.

A ɗaya ɓangaren ƙungiyoyi masu yaƙin kare haƙƙin bil adama sun fara kiraye-kirayen a bincika domin gano yadda aka yi mawaƙan suka samo takardun zama ‘yan ƙasar, kasancewar sun samo takardun ne a wasu wuraren kafin su zo wajen da za a yi musu fasfo, tare da kiran a yi musu adalci.

Babban mai shigar da ƙarar ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ana neman belinsu kan sefa (CFA) ta Nijar miliyan 10, ya ce har yanzu babu wata takarda da ke nuna hakan, kuma a cewar sa idan ma ta zo, to hakan ba zai taɓa tabbata ba sai da amincewarsa ko akasin haka.


Comments

One response to “Yadda aka kama Mr 442 da abokinsa da takardun bogi a Nijar”

  1. Su cigaba da rike su kawai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *