Matar da ake zargi da kisan yarinya a Jos ta shiga hannu

0
293

Daga Maryam Sulaiman, Abuja

Matar da ake zargi da kisan Yarinya a Jos ta shiga hannuJami’an rundunar ‘yan sandan jihar Filato sun kama Misis Nneamaka Nwachukwu da ake zargi da laifin azabtar da wata yarinya mai suna Margaret Joshua mai shekaru 11wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa, wacce aka kashen ‘yar asalin jihar Kebbi ce ta gudu ne saboda rashin tsaron da ke addabar yankin da take, kafin a kai ta wurin wanda ake zargin, wacce ta nemi a taimaka mata.

Bayanai sun nuna cewa yarinyar a lokacin zamanta da wanda ake zargin ba a sanya ta makaranta ba, kuma ana azabtar da ita akai-akai har sai da ta mutu sakamakon hakan. An kuma yi zargin cewa bayan da aka yi mata dukan kawo wuƙa a kwana kwanan nan, an tilasta ta zauna a cikin roba mai dauke da ruwan zafi, hakan yayi sanadiyar ƙonewar gaban ta, kuma ta rasu a asibiti a ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba.

Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta ƙasa reshen jihar Filato, Grace Pam, wadda ofishinta ke bin diddigin lamarin ta shaida wa jaridar Vanguard cewa, bisa la’akari da yawan tabo da raunukan da ke jikin yarinyar dole ne masu kula da ita sun yi ta gallaza mata a lokacin da take tare da su. “Ma’aikatan asibitin sun kira ni akan lamarin a ranar Litinin da ta gabata, inda suka shaida cewa Misis Nneamaka Nwachukwu ta yi wa wata yarinya ‘yar shekara 11 mummunan duka tare da raunata ta.

“Yarinyar tana da tabo da kuna a jikinta, an gaya mana cewa an kai ta asibitin Mandela da ke Kaduna kafin a tura ta zuwa Jos. “Lokacin da wasu ma’aikatanmu suka gana da matar da ake zargin a ofishin ‘yan sanda da ke Vom inda aka tsare ta, ta amsa cewa tana yi mata dukan tsiya kuma ta yi ikirarin cewa yarinyar tana wasa da al’auran ta ne, don haka ta hukunta ta don ta daina.

Ta yi ikirarin cewa ba ta san me yake zuwa mata ba,lokacin da take dukan ta, saboda tana nadaman a duk lokacin da ta doke yarinyan” inji Pam Da take magana game da ƙonewar da ta yi a mazaunin ta, wacce ake zargin ta, ta shaida cewa yarinyar ta faɗa cikin ruwan zafi kuma ta fice daga gidan bayan faruwar lamarin na kusan awa 24.

Sai dai an gano cewa wani ya ga yarinyar da ta ji rauni a kan titi ya kai ta ofishin ‘yan sanda da ke Kaduna Vom. Daga nan sai jami’an tsaro suka kai yarinyar asibiti kafin su kira mai kula da ita Misis Pam ta nuna damuwarta inda take cewa, “ba a dauki matakin kula da yarinyar da ke cikin halin da take ciki ba har na tsawon sa’o’i 24, sai wani ya gan ta ya kai ta. ofishin ‘yan sanda.”

Bayanai sun nuna cewa wannan ba shi ne karon farko da da wadda ake zargin ke cin zarafin yarinyar ba, domin tun da farko ‘yan sanda sun gargaɗe ta da cin zarafin yarinyar tare da neman a mayar da yarinyar ga iyayenta. Matar da ake zargin bata taɓa ganawa da iyayen yarinyar ba, wanda suke jihar Kebbi, amma an ce suna magana da su ta waya.

Sai dai an mayar da shari’ar daga ofishin ‘yan sanda da ke Kaduna zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Jos yayin da ake ci gaba da bincike. Misis Nwachukwu kafin a kama ta, ta yi aiki a daya daga cikin Cibiyoyin Bincike da ke Vom, karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato a matsayin Likitan Kwayoyin Halitta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here