Har yanzu ba a ga gawar jami’ar DSS da ta hallaka kanta a kogin Legas–LASEMA

0
415

Matar da tayi tsalle ta faɗa ruwan kogi a Legas da yammacin ranar Alhamis, an bayyana sunan ta da Adetutu Adedokun, wacce ma’aikaciyar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ce.

A cewar direban taxi na Uber da ya ɗauko ta a lokacin da ta fice daga motar ta abka kogin, Adedokun ta samu saɓani da saurayinta, kuma ana zazzafan rigimar ne ta umarce shi da ya tsaya, sannan ta sauko daga motar, ta nufi layin dogo na gada ta faɗa cikin kogin.

Adetutu Adedokun

Ma’aikaciyar, a kimanin watanni huɗu da suka gabata, an ce ta samu yabo daga shugaban hukumar wato DG na DSS, a matsayinta na mafi kyawun jami’in yaƙi da makamai. An kuma bayar da rahoton cewa saurayin nata ya nemi aurenta makonnin da suka gabata.

Babban Sakatare na Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Jihar Legas ta LASEMA, Dokta Olufemi Oke-Osanyintolua wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an haɗa tawagar bincike da ceto domin gano gawarta. Jami’an hukumar da Ma’aikatan kashe gobara na jihar Legas da hukumar kula da hanyoyisn ruwa ta jihar Legas (LASWA) da jami’an hukumar DSS sun duƙufa domin nemo gawar matar.

Leave a Reply