Sauya takardun kuɗi zai Karya darajar Naira – Zainab Ahmed

0
497

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta soki shirin Babban Bankin Najeriya (CBN) na sauya wasu takardun kudi, tana mai cewa hakan zai iya karya darajar Naira.

Ministar ta bayyana wa Majalisar Dattawa cewa CBN bai shawarci ma’aikatarta kan sauya takardun kudin ba.

“Masu girma sanatoci, CBN bai tuntube mu a Ma’aikatar Kudi ba kafin daukar wannan mataki na sauya wasu takardun Naira ba, don haka ba za mu iya aron bakinsu mu ci musu albasa ba.

“Amma a matsayina na babbar jami’a a haskar tsare-tsaren kudi a Najeriya, wannan tsarin da ake shirin aiwatarwa a yanzu, na na matukar hadari ga darajar Naira a kasuwar canjin kudade.”

KU KUMA KARANTA: Za a daina amfani da tsoffin kuɗaɗen Najeriya a watan Janairu 2023

Ministar ta yi wannan jawabi ne a lokacin da take kare kasafin ma’aikatarta a gaban kwamitin Kudade na Majalisar Dattawa a Yau Juma’a.

Bayanin nata na zuwa ne bayan Sanata Michael Okpeyemi Bamidele, ya yi mata korafi cewa kwana biyu kacal bayan CBN ya sanar da shirin sauya takardun Naira 100 zuwa 1,000, amma farashin canjin Dala ya yi tashin gwauron zabo daga Naira 740 zuwa N788.

Idan ba a manta ba, ranar Laraba ne Gwmanan CBN, Godwin Emefiele ya sanar da sauya takardun kudin daga ranar 15 ga watan Disamba, 2022.

Leave a Reply