HOTO: Budurwar da aka ciwa zarafi a Nasarawa ta nuna raunukanta

Wata budurwa ‘yar shekara 20 mai suna Blessing Mathia ta nuna halin da ta samu kanta ciki sakamakon dukan da ƙawarta, Ella da ‘yan uwanta suka yi mata a jihar Nasarawa.

Daga cikin hotunan da aka saka, an nuna ɗaya daga cikin hannayenta ya kumbura. Haka kuma faifan bidiyo da ke nuna yadda ake dukanta da tsige mata kaya na ta yawo a shafukan sada zumunta.

KU KUMA KARANTA:Yan sanda na binciken cin zarafin budurwa da malamim jami’a yayi, bisa zargin ta ƙwacewa ‘yarsa saurayi

Rundunar ‘yan sandan ta cafke biyu daga cikin waɗanda ake zargin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *