Wani ɗalibi ɗan Najeriya mai suna Sani Aliyu mai shekaru 21 da ke karatu a Amurka ya mutu sakamakon wani jirgi me saukar angulu da yayi haya don fita yawon shaƙatawa da budurwa sa.
Sani ya rasu ne a daren ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba. Ɗalibin Jami’ar Kudancin Georgia yana fitowa daga cikin jirgin, wanda abokansa biyu suka suka tuƙa shi, se jirgin ya taho ya buga masa kai har sau biyu, a filin jirgin saman Statesboro-Bulloch County.
Aliyu da budurwarsa sun tafi Savannah da ke kusa, wanda ke da nisan mil 55 daga Statesboro, daga babban harabar jami’ar, inda yake karatu.
Jake Futch Coroner na Bulloch County ya gaya wa Statesboro Herald: “Sun tashi zuwa Savannah don tafiyar shaƙatawa, sun dawo, suka sauka a filin jirgin saman Statesboro, kuma budurwar tasa tayi gaba, shi yana baya, se jirgin yayi juyi yazo ya buge shi.”
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Tarayya ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da jirgin ya “Tsaya a kan tudu”. Jirgin yana dauke da fasinjoji hudu, matuƙin jirgin, mataimakin matuƙin jirgin, Aliyu da budurwarsa. Babu wani da ya jikkata, sede Aliyu da tsautsayi ya faɗa kansa.
Wani mai magana da yawun ofishin Sheriff na Bulloch County, Todd Hutchens, ya ce lamarin hatsari ne kuma babu wanda ke da laifi: “Babu wanda yake da laifin komai. Hatsari ne.” Jami’ar Kudancin Georgia ta karrama Aliyu, wanda ya kasance kwararre ne a fannin gudanarwa.
[…] Source link […]
[…] KU KUMA KARANTA: Dalibi ɗan Najeriya da ke Amurka ya mutu sanadiyar haɗarin da ya yi da wani jirgin haya […]