Matashi ya bayyana shi ya shaƙe mahaifiyarsa har lahira saboda ta kira shi da shege

0
490

Wani matashi ɗan shekara 18, Tope Momoh, ya amince ya shaƙe mahaifiyarsa mai shekaru 52, Stella, saboda ta kira shi da shege.

Momoh ya ce ya yanke shawarar amsa laifin da ya aikata bayan sati biyu da binne mahaifiyarsa saboda ya kasa samun sukuni da kwanciyar hankali. A cewar jaridar The Nation, an ce ya aikata laifin ne da tsakar daren ranar 6 ga Satumba, 2022, a Ikakumi Akoko, a jihar Ondo.

An gurfanar da Momoh a gaban wata Kotun Majistare ta Akure bisa tuhumarsa da laifin kisan kai kuma ya nemi a yi masa rahama. Ɗan sanda mai shigar da ƙara, Nelson Akintimehin, ya shaida wa kotun cewa ba a san musabbabin mutuwar mahaifiyar ba har sai da ɗanta ya amsa cewa shi ne ya kashe ta.

“Momoh a cikin ikirari nasa ya ce an tilasta masa ya shaida wa ‘yan uwansa cewa ya shaƙe mahaifiyarsa har lahira. Hakan ya faru ne lokacin da ta tada shi da tsakar dare, inda ta yi masa ruwan tsinuwa tare da kiran sa da shege.

“Akintimehin ya ce laifin ya ci karo da sashe na 319(1) na kundin laifuffuka, Cap 37, Vol. II Dokar Jihar Ondo, 2006. Momoh, a sanda aka basa izinin yin magana yace, “Ni ban samu nutsuwa ba tunda aka binne mahaifiyata. Don haka, ya zamar min dole in furta cewa ni na shaƙe ta har ta mutu. Don haka ina so kotu ta tausaya mani.”

Ba a sauƙaka masan ba, amma Alƙalin kotun, Musa Al-Yunnus, ya bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali na Olokuta sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga Oktoba, 2022.

Leave a Reply