Ma’aikatar ayyuka ta Najeriya ta shawarci masu motoci su kauce wa titin Lokoja zuwa Abuja

0
269

Ma’aikatar kula da ayyuka da gidaje ta Najeriya ta buƙaci masu motoci da ke tafiya zuwa arewacin ƙasar daga yankin kudu ko gabashin ƙasar da su ƙaurace wa titin Lokoja zuwa Abuja.

Babban jami’in da ke kula da ayyuka na ma’aikatar a jihar Kogi Injiniya Jimoh Kajogbola, shi ne ya bayar da shawarar a wata sanarwa inda ya yi kira ga matafiyan da su yi amfani da wasu hanyoyin. Kiran ya biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye wasu sassan titin ne a yankin Koton-Karfe bayan da Kogin Kwara ya tumbatsa.

A sanarwar, jami’in ya shawarci masu motocin da za su je Abuja daga kudu maso yamma su bi ta titin da ya tashi daga Ilori ya bi ta Mokwa ya wuce ta Bida. Su kuwa matafiya daga yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu an shawarce su da su bi ta titin Makurdi zuwa Lafia.

Sanarwar ta buƙaci masu motocin da suma suke daga arewacin ƙasar da su bi waɗannan hanyoyin da aka bayar da shawarar masu fitowa daga yankin kudun zuwa arewa su bi, har zuwa lokacin da ruwan ya ja baya. Jami’in ya shawarce su da su bi titin Abuja zuwa Lafia ya wuce ta makurdi zuwa Otukpa ko kuma wanda titin Abuja zuwa Bida ya bi ta Mokwa ya wuce ta Jebba.

Wannan matsala ta ambaliya a titin na Lokoja zuwa Abuja ta haddasa matsalar ƙarancin mai a yankin babban birnin tarayya Abuja, kasancewar motocin dakon mai ba sa iya wucewa.

Leave a Reply