Hukumar kula da tallace-tallace ta Najeriya ta ce ta shigar da ƙarar kamfanin Meta mamallakin Facebook da Instagram da WhatsApp da wakilinsa kamfanin AT3 Resources Limited a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, hukumar ta ce ci gaba da wallafa tallace-tallace ga masu bibiyar Facebook da Instagram a Najeriya ba tare da tabbatar da samun amincewa kafin fitar da su ba, haramun ne, kuma take dokar tallace-tallace ce ta Najeriyar, kamar yadda BBC ta rawaito.
Hukumar ta ce kamfanin Meta ya ci gaba da yaɗa irin wadannan tallace-tallace da suka jawo wa gwamnatin tarayya asarar kuɗaɗen shiga.
Hukumar tana neman kamfanin na Meta ya biya tarar naira biliyan 30 kan take dokokin tallace-tallace da ya yi.