An yi jana’izar shahararren ɗan wasan Hausa Umar Malumfashi (Ka-Fi Gwamna) a Kano

0
565

Shahararren Ɗan wasan Hausa, wanda a da aka fi sani da Bankaura, a yanzu kuma aka fi sani da Kafi Gwamna ya rasu. Umar Malumfashi ya rasu bayan rashin lafiya da ya yi fama na tsawon lokaci.

A ‘yan kwanakin baya, jama’a sunga wani roƙon addu’a da Bankauran ya yi ga masoya da su taya shi da addu’ar samun lafiya.

Anyi jana’izar sa a jihar Kano, inda mutane da dama suka halarta. Jaruman kannywood sun zo da dama, don yima iyalinsa jaje da addu’a.

Bankaura yana cikin manyan ‘yan fina-finan Hausa da suka bayar da gudummawarsu ga masana’antar Kannywood na tsawon shekaru.

Leave a Reply