Osinbajo zai wakilci Najeriya a jana’izar Sarauniya Elizabeth a Landan

1
236

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bar Abuja yau, kuma zai wakilci Najeriya a jana’izar Sarauniya Elizabeth ta biyu a birnin Landan.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasa, Laolu Akande, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 17 ga Satumba, 2022. A cewar kakakin, mataimakin shugaban ƙasar zai kasance cikin manyan baƙi da Sarki Charles III zai tarbe shi a liyafar da za ayi a fadar Buckingham ranar Lahadi, da kuma jana’izar da za ayi ranar Litinin.

Ya kuma bayyana cewa, a gefen jana’izar akwai shirin ganawa da sakataren harkokin wajen Birtaniya, James Cleverly. Wani ɓangare na sanarwar yana cewa: “Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, SAN, zai wakilci Najeriya a wasu abubuwa a gobe da kuma Litinin, yayin da ake jana’izar marigayiya Sarauniya Elizabeth ll ta Burtaniya.

Farfesa Osinbajo ya bar Abuja a yau kuma zai haɗu da ‘yan gidan sarauta, da shugabannin ƙasashen duniya da suka haɗa da ‘yan kungiyar Commonwealth, shugabannin Kasashe, gwamnonin jihohi, firaministan ƙasar, da kuma iyalan sarakunan ƙasashen waje. A wajen bukukuwan, ciki har da bikin jana’izar da aka shirya yi a Westminster Abbey ranar Litinin.”

1 COMMENT

Leave a Reply