Zamu sayar da kadarorin gwamnatin tarayya don neman mafita- Ministar kuɗi

0
401


Daga Saleh INUWA, KANO
Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Kuɗi, Zainab Shamsuna Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya zata karɓi sabon bashin sama da Naira Triliyan 11 tare da sayar da kadarorin gwamnati don kasafin kudin 2023.


Ta bayyana cewa gwamnati zata buƙaci kudi N12.42 Trillion idan har zata cigaba da biyan tallafin mai a 2023.
Hajiya Zainab ta bayyana hakan ne ranar Litinin yayinda ta bayyana gaban yan majalsar wakilai a birnin tarayya Abuja.
Ta yi bayanin cewa zaɓi biyu gwamnati ke da shi, na farko a cigaba da biyan kuɗin tallafin mai a 2023 gaba dayya ko kuma a biya na watanni shida kaɗai zuwa bayan zabe.
A cewarta, idan aka biya kuɗin har ƙarshen shekara, ana buƙatar N12.41 Trillion a 2023. Amma idan zuwa watan Yuni bayan zabe zaa biya, N6.72 trillion zaa kashe kan tallafin mai.


Ta ƙara da cewa, da kamar wuya a iya biyan kuɗin tallafin gaba ɗaya duba da halin da ake ciki yanzu, amma idan aka biya na watannin shida kaɗai da ɗan sauki. A cewarta, idan aka biya na wata shida, zaa iya karɓan bashin N9.32 trillion don cikasa kasafin kudin 2023.

Leave a Reply