Matashi ya rasa ransa sakamakon faɗawa kogi a jihar Kano

Daga Shafaatu DAUDA, kano

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani matashi ɗan shekaru 25, mai suna Ammar Ibrahim a cikin wani Kogi a yankin ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Bayanin hakan ya fito ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Laraba Kano, inda ya rabawa manema labarai.

“Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:34 na safe daga wani mutumi Muhammad Sani kuma mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:55 na safe, inda suka bayar da agajin gaggawa, “inji PFS Saminu.

Hakazalika Saminu Yusif ya kuma ce, matashin ya nutse ne a cikin wani kogi a ƙauyen Tattarawa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, kamar yadda Jaridar Neptune prime ta rawaito.

Ya kuma ce, “Direban baburin Adai-daita Sahun da ke kan hanyarsa ta komawa Kano, ya tsaya ne a gefen titi kusa da wani kogi da nufin wanke babur ɗin, amma sai tsautsayi ya ja shi cikin kogin, wanda ya rasa ransa a ciki, “A cewar Saminu Yusif.

Jaridar Neptune prime ta rawaito cewar, Kakakin Hukumar kashe Gobarar Saminu Yusif ya ƙara da cewar, Matashin ya yi ƙoƙari wajen ganin ya tseratar da kan sa a cikin ruwan amma hakan bai yiwu ba.

Sannan kuma ya ce an fito da marigayin Ibrahim daga cikin ruwan a sume daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa, wanda aka miƙa gawar tasa ga Sifeto Jerry Mathew na ofishin ‘yan sanda na Dawakin Tofa a jihar Kano.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *