Jami’an tsaron Najeriya sun cafke wasu mutane huɗu da ake zargin na kwarmata bayanan sirri ga ‘yan bindiga a babban birnin ƙasar, Abuja.
Jaridar PRNigeria ta rawaito wata majiya mai ƙarfi ta hukumar leƙen asiri ta ƙasa da ke tabbatar da kamen.
An cafke mutanen tare da wasu na’urori da makamai da tsoffin wayoyin hannu da basa amfani da intanet.
Majiyar da ke cikin ayarin mutanen da suka yi kamen na cewa, ana ci gaba da bincike cikin sirri domin gano shugabanninsu da masu daukar nauyinsu.
Waɗannan mahara ake kuma zargi da kai hari a wasu sassan yankunan Abuja, a cewar majiyar.
Yanzu haka ana tsare da mutanen da aka cafke da tuhumarsu domin amsa tambayoyi.