Arewa ce koma baya wajen rajistar katin zaɓe, Kwana 3 kafin INEC ta rufe

0
475

Kwana uku kafin rufe yin rajista gabanin zaben 2023, ’yan Najeriya da dama da shekarunsu suka kai na zabe a Arewacin Najeriya ba su yanki katin zaɓe ba.

Alƙaluman masu katin zaɓe da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar sun nuna yankin Kudancin Najeriya ya yi wa Arewa fintinkau wajen yawan masu rajista, duk da cewa Arewa ta fi yawan al’umma.

BUƊE WANNAN BIDIYON DON GANIN AMFANIN KATIN ZAƁE: https://youtu.be/lEoxTkZh5ZQ

Jihar Legas ce a kan gaba da mutum 508,936, sannan jihohin Kano a matsayi na biyu, Delta ta uku, ta hudu Ribas, sai Kaduna sannan Bayelsa.

Hakan  kuwa ta faru ne duk da cewa, a kwanakin baya, INEC ta ƙara wa’adinta na rufe rajistar zaben daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa ranar 31 ga watan Yuli.

A wasu jihohin har hutu gwamnatoci suka bai wa ma’aikata domin su samu yin rajistar; Wasu wuraren ibada ma sun wajabta wa mabiyansu yin rajitsar.

A ranar 28 ga watan Yunin 2021 hukumar ta ƙaddamar da aikin ci gaba da rajistar katin zaɓen domin sabunta wanda ake da shi gabanin babban zaɓen 2023.

Amma yanzu da ya rage kwana uku a rufe, alƙaluman Hukumar sun nuna yawancin masu zaɓe ba su yi ba.
Masu lura da al’amuran yau da kullum sun alaƙanta matsalar a Arewacin Najeriya da matsalar tsaro da kuma ɓacin ran masu zabe da kamun ludayin zaɓaɓɓun shugabanni.

Leave a Reply