Mutane na fatan mushiga wuta – Hauwa Waraka

0
243

Daga Saleh Inuwa, Kano

Ficacciyar jarumar fina-finan hausa ta masana’antar kannywood, Hauwa Waraka, ta bayyana cewa mutane da dama kallon ‘yan wuta suke yiwa ‘Yam Fim.

Jaruma Hauwa Waraka

Har ma take cewa, da mutane suna da makullin Wuta ko na Aljanna to da Wuta zasu na kaiwa galibin ‘Yam Fim.

Sai dai kuma jarumar ta ce, hakan sam ba ya ɓata mata rai sabida ta san babu mai Wuta da Aljanna sai Allah, kamar yadda shafin Hauwaloaded suka ruwaito.

Jaruma Hauwa Waraka ta bayyana hakan ne a wata hirarta da sashen BBC Hausa a cikin shirinsu mai suna Daga Bakin Mai Ita.

Jaruma Hauwa Waraka

A cewarta, “Ni abin da nake fada wa al’umma na san mutum dai ba shi da mukullin Wuta ba shi da na Aljanna bare ya ce ai ni ne mai makullin Wuta, Wutar zan kai ki ko kuwa ni ne mai makullin Aljanna Aljanna zan kai ki”.

Don akasarin mutane kallon da suke yi mana da su suke ba da Wuta da Aljanna da ba za su ba dan fim Aljanna ba, magana ta gaskiya sabida kallon da suke mana.

Sabida akwai mutanen da za ka ji ko sunana aka kira sai ka ji sun ce wannan makamashin wutar?, To ni kuma na ga ba ka da Wuta ba ka da Aljanna Allah ne yake ba da ita ba mutum ba.

Ni kuma na san wacece ni na san tsakanina da Ubangiji kuma na san zuciyata, shi ya sa ni duk abin da mutum zai fada wallahi ba ya damu na.

Da aka tambayeta dalilin da yasa take fitowa a matsayin wacce ba mutuniyar kirki ba a fim sai jarumar ta ce, a zahiri ba haka take ba suna yi ne don su fadakar da masu yin halin don su daina.

Ni ga duk lokacin da aka sa min kyamara ba na jin nauyin komai amma na san dai kamar busa sigari ko gidan karuwai, irin abubuwan da suke yi na san a addininmu da al’adarmu ba kyau.

Amma kuma muna yi ne don mu fadakar da masu yi kan illar abin cewa ba abu ne mai kyau ba.Shi ya sa idan za’ nuna irin wadannan matan dole sai an nuna irin abin da suke yi dalilin da ya sa ake ba mu irin wannan muna yi, amma ba wai da gaske ba ne ni a zahiri babu abin da nake sha, cewar jaruma Hauwa Waraka.

Leave a Reply