Matar Marigayi Abba Kyari ta zama Gimbiya ta farko ta Masarautar Jama’are

0
427

Sarkin Jama’are, Alhaji Nuhu Muhammadu Wabi, a ranar Lahadi ya naɗa matar tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, marigayi Abba Kyari, Hajiya Hauwa Kulu Abba Kyari a matsayin ‘Gimbiya ta Jama’are’ ta farko. Da yake jawabi a wajen bikin rawani a fadarsa, Sarkin Jama’are, Nuhu Muhammadu Wabi ya bayyana ta a matsayin ‘yar Jama’are ta gaskiya wadda ta yi ƙoƙari wajen ci gaban Masarautar baki daya.

A cewar Sarkin, aikin Gimbiya na gargajiya shi ne ya zama wata gada tsakanin Sarki da matan da ba su da ra’ayin kai tsaye a cikin al’amuran gargajiya, “Tare da rawani a matsayin Gimbiya, matan Jama’are yanzu sun samu wakilai a Majalisar Masarautar, yanzu ana iya jin muryoyinsu ƙarara”.

“Na cika cewa a yanzu ina da ‘yar Masarautar ta gaske a Majalisar, mace ce mai zuciya da ta damu da jin dadin jama’arta da kuma ci gaban masarautar,” inji shi. Sarkin ya ce, “Duk da cewa ta bayar da gudunmawar abubuwa da dama wajen ci gaban Masarautar Jama’are, da wadannan muna sa ran fiye da haka, wannan shi ne aikin da ke wuyanta a yanzu”.

A taƙaitaccen jawabin da ta yi bayan an yi rawani, Gimbiya ta farko ta Jama’are, Hauwa Kulu Abba Kyari ta gode wa Sarkin bisa yadda ya same ta da wannan karramawa wanda ya zo mata da mamaki.

Ta jaddada ƙudirinta na ci gaba da bayar da gudummawar kasonta don ci gaban Masarautar da jama’ar Jama’are wadanda ta ce sun yi tasiri sosai a rayuwarta, ta kuma nuna farin cikinta da karramawar da akai mata, wanda tace yazo mata ne ba tsammani.

A martanin da ya mayar dangane da wannan rawani, Manajan Daraktan Rukunin Kamfanin na NNPC, Mele Abba Kyari ya yi mata fatan alheri inda ya ce kira ne a gare ta da ta ƙara himma wajen ci gaban Masarautar Jama’ar da kuma bil’adama baki daya. “Muna nandin taya ‘yar’uwar da ta yi kyakkyawan aiki ga bil’adama kuma ta cancanci a gane haka”.

Leave a Reply