Zaizayar ƙasa ta lalata gadar da ta haɗe unguwannin Sheka da Gurungawa a Kano

Daga Shafaatu Dauda, Kano

Al’ummar unguwanin Sheka da Gurungawa dake ƙaramar hukumar Kumbotso ta Jihar Kano, Sun koka akan lalacewar wata gada data haɗa unguwannin guda biyu, dayanzu haka ruwan damina ya zaizaye ta, sakamakon rashin kyawun hanyar, domin ba a taba zuba mata kwalta ba.

zaizaye

Wasu daga cikin mutanan unguwannin sun ce, hanyar ita ce daya tilo da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum, wanda a yanzu ruwan daminar ya zaizaye wasu ɓangarori na hanyar.

Sunyi kira ga gwamnatin Jihar Kano, da mahukunta na ƙaramar hukumar da su kawo musu daukin gaggawa dan gyara hanyar, wadda dimbin al’umma ke amfana da ita akoda yaushe.

Gadar da ruwa ya ci

Hanyar dai ta tasone daga Sheka unguwar kudu, wadda ta tafi Gurungawa. Mazauna garin sunce dama gadar, tsohon dan majalisar dokokin jihar Kano ne, Hon. Naziru Zakari Sheka ya samar musu da ita abaya, amma sakamakon rashin fitar da magudanan ruwa, da zuba kwalta akan hanyar, yasa gadar take zaizaya.

Jaridar Neptune Prime ta tuntubi dan majalisar dokokin Jihar Kano dake wakiltar al’ummar ƙaramar hukumar Kumbotso, Hon.Mudassir Fanshekara ta wayar Salula, domin jin ta bakinsa akan yunƙurin da suke yi na samar wa al’ummar wadannan yankuna mafita, Sai dai, haƙarmu bata cimma gaci ba, sakamakon wayarsa bata shiga.

Jaridar Neptune Prime ta samu damar daukar hotunan wasu ɓangarori na gadar daya rufta, da kuma wasu manyan ramuka da zaizayar ruwan ya haifar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *