Gidajen burodi da dama sun rufe a Abuja, saboda tsadar kayan aiki

0
306

Aƙalla gidajen burodi 40 ne suka rufe shagunansu a babban birnin tarayya Abuja, saboda tsadar kayayyakin aiki, da kuma yawan haraji, tare da ƙarin kudin wutar lantarki da dai sauransu.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa wasu gidajen biredin da suka ziyarta, ba a bude su ba don kasuwanci, saboda tsadar kayan aiki dana haraji da wasu hukumomin gwamnati ke yi.

Wasu daga cikin gidajen burodin da suka rufe sun hada da Abumme bakery Ltd. Lugbe, titin Airports, Hamdala Bakery, Kuje, Harmony Bite Bakery, Karu, Doweey Delight Bakery Ltd, Kubwa. Sauran sun hada da Merit Baker, Mpape, Funez Baker, Orozo, Slyz Bakery, Wuse Zone 2, da sauransu.

Mista Ishaq Abdulraheem, shugaban kungiyar masu yin burodi a Abuja, babban birnin tarayya, ya ce abin na kara tada hankali yadda gidajen burodin da ke Abuja ba za su iya jurewa tsadar kayan da ake aiki dasu ba.

Ya ce akasarin ‘yan kungiyar sun rasa abin dogaro da kai, yayin da ma’aikata suka rasa aikin yi saboda rufewar da aka yi.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta shiga tsakani, ta kuma duba hukumomin gwamnati da ke kawo cikas ga harkokin kasuwancin biredi. Ya bayyana wasu daga cikin hukumomin da suka hada da Hukumar Kula da Magungunan Abinci ta Kasa (NAFDAC), Standard Organisation of Nigeria (SON), National Environmental Standards and Regulations, National Environmental Standards and Regulations, National Enforcement Agency (NESREA).

Wani mai biredi a Abuja, Mista Nuhu Musa na Hamdala Bakery, Kuje, FCT, ya roki gwamnati da ta daidaita ayyukan wadannan hukumomi don rage haraji daban-daban da suke sanyawa masu yin burodi.

Musa ya ce, gidajen biredi da dama na kokawa da rayuwa saboda tsadar sarrafawa. “Muna son gwamnati ta daidaita wadannan hukumomi ta yadda ayyukanmu za su kasance cikin sauki. “Wadannan harajin suna yin mummunar tasiri ga kasuwancinmu har ya kai ga yawancin mu sun rufe. Wannan kuma yana shafar ayyukan yi domin da yawa daga cikin ma’aikatan biredi ba su da aiki a halin yanzu, kuma kun san tasirin hakan ga al’umma; wasu za su koma aikata laifuka,” inji shi.

Musa ya ce, alal misali, NAFDAC za ta zo gidajen burodin su don duba takardun shaida, yayin da SON za ta zo a yi rajistar kayayyakin. “Nawa muke bayarwa don ba da garantin duk waɗannan dubawa da biyan kuɗi,” in ji shi.

Wasu mazauna yankin da suka zanta da NAN sun koka kan tsadar biredi a kasuwar, inda suka jaddada cewa a hankali biredi ya zama abincin masu hannu da shuni. Mista Julius Anthony, wani mazaunin garin ya ce wasu daga cikin biredin da ya saba saya kan Naira 500 kan kowane bulo yanzu sun kai Naira 1,000.

Wata matashiya Aisha Danjuma,  mazauniyar babban birnin ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta shiga tsakani kan tsadar biredi, inda ta kara da cewa “bread abincin talakawa ne kuma ba za a kwace musu ba.” (NAN)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here